Iraqi-Iran

Majalisar dokokin Iraki ta zabi sabon shugaba.

Le nouveau président du Parlement irakien, Mohamed Al-Halboussi, le 15 septembre 2018.
Le nouveau président du Parlement irakien, Mohamed Al-Halboussi, le 15 septembre 2018. AFP

A yau majalisar dokokin kasar Iraki ta zabi shugabanta, dan takarar dake samun goyon bayan yan majalisun da Iran ke goyawa baya, matakin da ya buda hanyar kaiwa ga gafa gwamnati watanni 4 bayan gudanar da zaben yan majalisar dokokin.

Talla

A wannan lokaci da kasar ta shiga rudu, tun bayan zaben na watan mayun da ya gabata, ana sa ran dai, ‘yan majalisar dokokin su zabi mataimaka 2 ga shugaban Majalisar, wanda hakan zai kara tabbatar da kawancen da aka yi tsakanin jam’iyu a majalisar.

Ana dai ganin gungun yan majalisun da Iran ke goyawa, karkashin kawancen Hadi al-Ameri, na mayakan da suka yi jidali da kungiyar Isis a karkashin tallafin kasar Iran, ya kama hanyar zama kan gaba a siyasar kasar ta Iraki, bayan zaben dan takarsa a shugabancin majalisar dokokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.