Philippines

Mutane da dama ne suka mutu a Philippines

Yankunan Pangasinan, Tarlac, Pampanga da Bulacan,na Manilla na kasar Philippines
Yankunan Pangasinan, Tarlac, Pampanga da Bulacan,na Manilla na kasar Philippines REUTERS

Hukumomin Philippines sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon guguwar da ta afkawa kasar ya kai 74 yanzu haka, yayin da masu aikin agaji ke amfani da tafin hannun su wajen tono domin ko zasu gano wadanda suka tsira da rayukan su.

Talla

Guguwar wadda itace mafi girma da ta afkawa yankin daban ta lalata gidaje ad haifar da ambaliyar da ta mamaye gonaki a arewacin Philippines kafin ta isa Hong Kong da China.

Ya zuwa yanzu akalla mutane 40 ake zaton zabtarewar kasa ta birne a Itogon, daya daga cikin yankunan da aka samu matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.