India

Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India

Matan Musulmi a India sun yi maraba da dokar haramtawa magidantansu yi musu saki uku a lokaci guda.
Matan Musulmi a India sun yi maraba da dokar haramtawa magidantansu yi musu saki uku a lokaci guda. Asia Times

Gwamnatin India, ta sanya hannu kan dokar haramtawa magidanta Musulmi furta kalaman saki uku ga mata a lokaci guda.

Talla

Tun a watan Agustan da ya gabata, bangaren zartaswa ya mika kudurin dokar haramta saki ukun a lokaci guda ga zauren majalisar kasar ta India, wanda ya gaza samun amincewar ‘yan majalisun.

Rashin amincewar majalisar ne yasa gwamnatin India ta yi amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya bata, wajen zartar da kudurin a matsayin doka, wadda ta soma aiki nan take.

A karkashin dokar, duk wani Musulmi dan kasar India da aka samu da lafin yiwa matarsa saki uku a lokaci guda, zai fuskanci hukuncin daurin shekaru uku a kurkuku tare da biyan tara.

A shekarar 2017, Fira Ministan India Narendra Modi ya fito da kudurin baiwa mata Musulmi na kasar kariya kan hakkokinsu na auratayya, sai dai rashin samun rinjayen da ake bukata a zauren majalisar kasar ya hana kudurin soma aiki a matsayin doka.

Daya daga cikin sassan dokar da masu adawa da ita ke suka, shi ne rashin bada damar yin belin magidantan da aka kama da laifin na yiwa matansu saki uku a lokaci guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.