Iran-Amurka

Iran ta yi watsi da tayin Amurka

Iran ta yi watsi da tayin cimma sabuwar yarjejeniyar da Amurka ta yi mata a jiya Alhamis, inda tace Amurkan ta karya ka’idojin muhimmiyar yarjejeniyar nukiliya da suka kulla tare da wasu manyan kasashe a 2015.

Hassan Rouhani shugaban kasar Iran
Hassan Rouhani shugaban kasar Iran Kirill Kudryavtsev/Pool via REUTERS
Talla

Minstan harkokin wajen Iran, Javad Zarif, ya ce Amurka ba son zaman lafiya take ba, la’akari da sabbin bukatun da take shirin bijiro da su, musamman kan shirin kera manyan makamai masu linzamin Iran da kuma siyasar ta a gabas ta tsakiya.

A wata ganawa da Kamfanin dillacin labarai na Tasnim a kasara Iran a yan watanni da suka gabata Mohammad Javad Zarif Ministan harakokin wajen Iran  ya nanata matsayar kasar Iran na cewa babu batun wata tattaunawa da Amurka haka zalika sun yi watsi da duk wani tayin Amurka kan tattaunawa da Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI