Yemen

Jami'an agaji na fuskantar koma baya a Yemen - MDD

Shugaban hukumar bada agajin jin kai na Majalisar dinkin Duniya Mark Lowcock ya ce jami’an agaji suna fuskantar koma baya sosai, dangane da fafutukar da suke na kawo karshen yunwa a kasar Yemen.

Daya daga cikin kananan yaran dake fama da yunwa a kasar Yemen.
Daya daga cikin kananan yaran dake fama da yunwa a kasar Yemen. REUTERS/Khaled Abdullah/File Photo
Talla

Lowcock yayi gargadin cewa nan da kankanin lokaci akwai fargabar samun karin ‘yan kasar ta Yemen akalla miliyan 3 da rabi da za su fada cikin bala’in yunwa, kari kenan akan ‘yan kasar miliyan 8 da suka dade cikin wannan mayuwacin hali, sakamakon kazamin yakin da ake fafatawa tsakanin Saudiya da 'yan tawayen Houthi da suka hambarar da gwamnatin kasar.

A halin da ake ciki yanzu, majalisar dinkin duniya da sauran masu shiga tsakani da ke kokarin jagorantar tattaunawar sulhu a Geneva, sun yi nasarar tsagaita yakin da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen Houthi da rundunar kasashen larabawa bisa jagorancin Saudiya har na tsawon watanni 11, domin lalubo bakin zaren kawo karshen yakin kasar Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI