Iran

'Yan bindiga sun bude wuta kan sojin Iran dake fareti

Wasu dakarun kasar Iran yayin gudanar da fareti.
Wasu dakarun kasar Iran yayin gudanar da fareti. AFP/STRINGER

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan sojin Iran da ke gudanar da fareti a yankin kudu maso yammacin kasar, da safiyar yau Asabar, inda suka hallaka sojoji 8 tare da jikkata wasu mutane 20.

Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Iran ya rawaito cewa an kai harin ne a garin Ahvaz, inda dakarun kasar ke tunawa da zagayowar ranar da yakin tsawon shekaru 8 da ya barke tsakaninsu da Iraqi, a zamanin gwamnatin Saddam Hussein a shekarar 1980.

Kafafen yada labaran kasar ta Iran sun rawaito cewa ‘yan bindiga biyu ne suka bude wuta kan dandazon jama’ar da suke kallon yadda faretin sojin ke gudana a garin na Ahvaz, daga bisani kuma suka juya da nufin bude wuta kan sashin manyan bakin da ke halartar taron, sai dai basu samu nasarar hakan ba, jami’an tsaro suka maida musu martani, inda suka jikkata su.

An dai gudanar da faretin na tunawa da ranar da kasar ta Iran ta soma yaki da Iraqi a zamanin shugabancin Saddam Hussien a mafi akasarin manyan garuruwan kasar ta Iran.

Duk da cewa ba sabon abu bane hare-haren da ‘yan tawayen Kurdawa ke kaiwa jami’an tsaron Iran a kan iyakokin kasar, ba a saba ganin irin wannan hari a manyan garuruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.