Iran

Amurka na kokarin haddasa fitina a kasarmu - Rouhani

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani. © REUTERS/Lisi Niesner/File Photo

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sha alwashin mayar da zazzafan martani kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kaiwa taron faretin dakarun kasar a jiya Asabar, inda mutane 29 suka hallaka, wasu 57 kuma suka jikkata.

Talla

Bikin faretin na gudana ne a garin Ahvas da ke kan iyakar Iran daga bangaren kudu maso yammaci, da Iraqi, kuma an saba bikin don zagayowar, ranar da aka soma yaki tsakanin Iraqi da Iran, da aka shafe shekaru 8 ana gwabzawa, a zamanin mulkin marigayi Saddam Hussein.

Duk da cewa kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin, shugaban kasar ta Iran, Hassan Rouhani ya zargi Amurka da cewa ita ce ke shirya haifar da matsalar rashin tsaro a kasar.

Kafin barin birnin Tehran zuwa New York domin halartar taron shugabannin kasashen duniya a zauren majalisar dinkin duniya, Shugaban na Iran ya kuma zargi wasu kasashen Larabawa a yankin Gabas ta Tsakiya da baiwa kungiyoyin ‘yan ta’adda kudade da makamai, domin haddasawa Iran matsalolin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI