India

Likitocin India basa iya gano tarin fuka-Bincike

Likita na bincinken gano  alamar cutar tarin fuka
Likita na bincinken gano alamar cutar tarin fuka Cris BOURONCLE / AFP

Wani Bincike da aka gudanar a kasar India ya nuna cewar akasarin likitocin dake aiki a asibitin kudi basu iya gani masu fama da cutar tarin fuka domin basu maganin da ya dace da su.

Talla

Rahotan wanda ya bayyana cutar a matsayin daya daga cikin manyan cututtukan dake barazana ga jama’a a kasashen India da China da Indonesia, ya ce mutane sama da miliyan 1 da 700,000 suka mutu sakamakon cutar, kamar yadda alkaluman hukumar lafiya suka tabbatar.

Binciken da Jami’ar McGill ta gudanar da tallafin Bill da Melinda Gates tare da Bankin Duniya da Jami’ar John Hopkins yace akasarin likitocin basa iya gane alamar cutar lokacin da ta fara a binciken da aka gudanar a biranen Mumbai da Gabashin Patna.

Binciken da aka wallafa a Mujallar Lafiyar The Lancet yace muddin ba’a dauki matakan da suka dace ba, nan da shekarar 2040 sama da kashi 12 na masu fama da cutar ba zasu samu maganin da zai warkar da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI