Syria

Rasha ta soma mikawa Syria manyan makamai masu linzami

Makami mai linzami kirar S-300, yayin gwajinsa a wajen garin Astrakhan, da ke Rasha. 5, Agusta, 2017.
Makami mai linzami kirar S-300, yayin gwajinsa a wajen garin Astrakhan, da ke Rasha. 5, Agusta, 2017. REUTERS/Maxim Shemetov

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce gwamnatinsu ta soma mikawa Syria, manyan makamai masu linzami kirar S-300, wadanda za’a iya amfani da su wajen kakkabo jiragen yaki.

Talla

Yayin sanar da matakin, Lavrov ya gargadi kasashen Turai, da su kaucewa duk wani yunkuri na haifar da cikas ga yunkurin da ake na kawo karshen kazamin yakin kasar ta Syria, wanda ya shafe shekaru 7.

Masu sharhi dai na ganin mallakar makamai masu linzamin na S-300, zai kawo karshen kutsen da jiragen yakin Isra’ila kan yi zuwa sararin samaniyar Syria da nufin kai farmaki, kan wasu yankunan da take ikararin tana fuskantar barazana.

Makwanni biyu da suka gabata ne rundunar sojin Isra’ila ta jajanta mutuwar ilahirin fasinjojin jirgin yakin Rasha da sojin Syria suka harbo, a lokacin da jiragen yakinta suka kai hari kan wasu cibiyoyin sojin Syrian.

Har ila yau Isra’ilar, ta dora alhakin aukuwar hadarin akan shugaban Syria Bashar al-Assad da kasar Iran.

Kalaman na Isra’ila sun zo ne jim kadan bayan zargin da Rasha ta yi mata, na yin amfani da jirgin yakinta a matsayin garkuwa a lokacin da ta kaddamar da wani farmaki akan wata cibiyar ajiyar makaman Syria da kawayenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.