Myanmar-ICC

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi hukunta Myanmar kan 'Yan Rohingya

Wasu mutane 10 kenan 'Yan kabilar Rohingya da Sojin Myanmar suka kamo tare da azabtar da su a Jihar Rakhine.
Wasu mutane 10 kenan 'Yan kabilar Rohingya da Sojin Myanmar suka kamo tare da azabtar da su a Jihar Rakhine. ©To match Special Report MYANMAR-JOURNALISTS/TRIAL REUTERS/File

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa har yanzu ana ci gaba da kisan kare dangi kan tsirarun musulmi ‘yan kabilar Rohingya a wasu sassa na kasar Myanmar, matakin da majalisar ta bukaci shigar da shi gaban kotun hukunta manyan laifuka.

Talla

A zaman da majalisar ta gudanar Larabar makon nan, Tawagar Jami’anta karkashin jagorancin Marzuki Darusman da ke bincikar zargin kisan kare dangin kan ‘yan Kabilar ta Rohingya ta tabbatar da cewa har yanzu Mynamar na ci gaba da gallazawa tsirarun musulmin azaba baya ga yi musu kisan Kiyashi.

Marzuki wanda ya gabatar da wani rahoton tawagar gaban zaman kwamitin tsaro na Majalisar wanda kasashen yammacin turai suka shirya amma ya fuskanci kakkausar suka da China da Rasha, ya ce babu abin da ya sauya a cin zarafin da gwamnatin ta Myanmar ke yi ga musulmin ‘yan Kabilar Rohingya.

Rahotan ya kuma bukaci majalisar ta yi amfani da karfinta wajen gurfanar da Kwamandan Sojin na Myanmar Min Aung Hlaing tare da bincikarsa kan hannunsa a yunkurin shafe kabilar ta Rohimgya.

A cewar Darussalam yanzu haka Sojin Myanmar sun kashe fiye da muslmin ‘yan Rohingya dubu 10 tare da lalata akalla kauyuka 390.

Kawo yanzu dai Shugabar gwamnatin Myanmar Aung su kyi ta ki amincewa da zargin cewa da hannun jami’anta a kisan daruruwan musulmin baya ga tilastawa kusan miliyan tserewa daga kasar a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.