Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta bukaci mika mata wadanda ake zargi da hallaka Kashoggi

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. REUTERS/Tumay Berkin
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Turkiya ta bukaci Saudiya ta mika mata mutane 18 da ta kama, bisa zarginsu da hannu a kisan gillar da aka yiwa dan Jarida Jamal Kashoggi a osfishin jakadancinta dake birnin Istanbul.

Talla

Wani babban jami’in gwamnatin Turkiya yace kasar ta mika wannan bukata ce, la’akari da cewa, tsarin shari’arta shi yafi cancantar hukunta wadanda ake zargi da kisan gillar dai dai da abinda suka aikata.

Saudiya ta kame mutane 18 din da Turkiya k enema ne bayan soma fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, a dalilin kisan Jamal Kashoggi a ofishin jakadancinta a Istanbul, ranar 2 ga watan Oktoba, wanda ke aiki da Jaridar Washington Post kuma mai sukar masarautar kasar.

A Juma'ar nan ce shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya bukaci hukumomin Saudiya su gaggauta bayyana wanda ya bada umarnin kisan gillar da aka yi wa dan jarida Kashoggi, zalika su kuma yi karin bayani kan yadda aka yi da gawarsa.

Jawabin na Erdogan yazo ne a daidai lokacin da babban mai gabatar da kara na Saudiya ke shirin isa Istanbul a wannan Lahadi 28 ga watan Oktoba, dangane da batun gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yiwa Kashoggi, dan jaridar da yayi kaurin suna wajen sukar masarautar kasar ta Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.