Indonesia

Dukkanin fasinjojin jirgin saman Indonesia 189 sun hallaka

Wasu daga cikin jami'an ceto dake laluben gawarwakin fasinjojin jirgin saman Indonesia da ya fada cikin teku. (29/10/2018).
Wasu daga cikin jami'an ceto dake laluben gawarwakin fasinjojin jirgin saman Indonesia da ya fada cikin teku. (29/10/2018). REUTERS/Stringer

Jami’an ceto a Indonesia sun bayyana kyautata zaton cewa, baki dayan fasinjoji 189 na jirgin saman kasar da yayi hadari sun hallaka.

Talla

Jami’an sun bayyana fargabar ce, bayan gano wasu daga cikin ragowar sassan fasinjojin jirgin saman na Lion Air.

Shugaban tawagar aikin ceto da ke laluben gawarwakin fasinjojin Bambang Suryo Aji, ne ya tabbatarwa da manema labarai halin da ake ciki na yakinin hallakar ilahirin fasinjojin, sai dai yace jami’an ceto zasu su ci gaba da aiki tukuru wajen laulube.

A halin da ake ciki, akalla kwararrun masu linkaya 40 ne suka dukufa wajen kokarin laluba sashin tekun da jirgin saman ya fada, inda aka kiyasta zurfin wurin yana tsakanin mitoci 30 zuwa 40.

Jirgin kirar Boeing 737 wanda ya soma aiki a ‘yan watannin baya, ya bace ne bayan mintuna 13 da tashinsa daga filin jiragen sama na birnin Jakarta domin zuwa garin Pangkal Pinang inda ya sulmiya cikin tekun Java.

Ma’aikatar sufurin Indonesia ta ce jirgin da yayi hadari na dauke da manyan fasinjoji 178, karamin yaro daya da kuma jarirai biyu, sai kuma matuka biyu da wasu ma’aikatan jirgin guda shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.