Afghanistan

Mutane 23 sun hallaka a hadarin jirgin sojin Afghanistan

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin harbo jirgin sojin Afghanistan.
Kungiyar Taliban ta yi ikirarin harbo jirgin sojin Afghanistan. Dunya News

Wani jirgin saman sojin Afghanistan mai saukar ungulu yayi hadari a yankin yammacin kasar a wannan Laraba, inda baki dayan fasinjojin dake cikinsa suka hallaka.

Talla

Kakakin gwamnan lardin Farah Nasir Mehri ya ce jirgin sojin ya fadi ne a yankin Anar Dara a dalilin rashin kyawun yanayi.

Karin bayani daga jami’an gwamnatin Afghanistan sun ce jirgin ya yi karo da wani tsauni ne, abinda ya haifar da hadarin nasa, sai dai mayakan Taliban sun yi ikirarin cewa sun ne suka harbor jirgin kasa a lokacin da yake kan hanyar isa lardin Herat.

Jami’an agaji sun ce baki dayan fasinjoji 23 dake cikin jirgin sun hallaka, ciki harda wani mataimakin kwamandan sojin Afghanistan dake lura da yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.