Sri Lanka

Sirisena ya maido da Majalisar Dokokin Sri Lanka bakin aiki

Shugaban Sri Lanka Maithripala Sirisena
Shugaban Sri Lanka Maithripala Sirisena REUTERS/Dinuka Liyanawatte

Shugaban Sri Lanka, Maithripala Sirisena ya janye matakinsa na dakatar da Majalisar Dokokin Kasar, yayin da ya sanya ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar gudanar da wata ganawa da ‘Yan Majalisun, a wani yunkuri na magance rikicin siyasar da ya kunno kai tsakanin bangarorin da ke adawa da juna.

Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Sirisena ya nada tsohon shugaban kasa , Mahinda Rajapaksa a matsayin Firaminista bayan ya rusa gwamnatin Ranil Wickremesinghe da ya kora daga mukamin Firaminista.

A yayin jagorantar wani taro a babban birnin Colombo, Rajapaksa ya ce, shugaban kasar ya yanke shawarar dawo da Majalisar bakin aiki a ranar 5 ga wata.

Wannan matakin zai bai wa Mambobin Majalisa 225 damar zama don zaben wanda zai ci gaba da rike kujerar Firaminista tsakanin Rajapaksa da kuma Wickremensinghe .

Ana saran ‘Yan Majalisun su kada mafi yawan kuri’unsu ga wanda suke so a matsayin Firaminstan Sri Lanka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.