Pakistan

Musulmi a Pakistan sun dakatar da bore bayan cimma matsaya da gwamnati

Jama'a na sauraron jawabin Firaministan Pakistan Imran Khan game da neman zaman lafiya saboda bore da ake yi.
Jama'a na sauraron jawabin Firaministan Pakistan Imran Khan game da neman zaman lafiya saboda bore da ake yi. rfi

Kungiyoyin musulmi a kasar Pakistan sun sanar da jingine zanga-zanga da suke yi saboda hukuncin kotun koli na kasar da ta saki wata mace Kirista da ake zargi da yin batunci ga addinin musulunci.

Talla

Kwanaki uku aka kwashe ana kazamin zanga-zanga a fadin kasar, kuma kamar yadda shugabannin kungiyoyin musulmi na kasar ke cewa sun janye ne bayan wata yarjejeniya da Gwamnati.

Tun Laraba ake zanga-zanga a fadin kasar bayan da Kotun ta salami Asia Bibi wadda take tsare na tsawon shekaru  takwas tana jiran hukunci saboda aikata sabo.

Yanzu haka dai Lauyan dake kare Asia Bibi ya tsere daga kasar Pakistan saboda zargin ana barazana ga rayuwarsa.

Lauya Saiful Mulook ya kare Asia Bibi game da zargin da ake yi mata na yin sabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.