Syria

Agajin farko ya isa sansanin Rukban a Syria tun bayan na Janairu

Sansanin 'yan gudun hijira na Rukban da ke Syria a kusa da kan iyakar Jordan.
Sansanin 'yan gudun hijira na Rukban da ke Syria a kusa da kan iyakar Jordan. AP News

Tawagar jami’an agaji ta majalisar dinkin duniya, ta isa sansanin Rukban na ‘yan gudun hijirar Syria dake kan iyakar kasar ta Jordan a cikin hamada, mai dauke da akalla mutane dubu 50, wadanda dubu 18 daga ciki kananan yara ne.

Talla

Karo na farko kenan da irin wannan taimako na kayan abinci da magunguna ke isa ga ‘yan gudun hijira, tun bayan wanda suka samu a watan Janairun wannan shekara.

Kungiyar bada agajin Red Crescent dake Syrian ta ce, sama da manyan motoci 70 ne suka isa sansanin, dauke da kayan agaji, wadanda suka taso daga birnin Damaskas.

Ana sa ran yi wa kananan yara dubu 10 allurar rigakafin cutar kyanda ko bakon dauro a sansanin 'yan gudun hijirar da suka shafe watanni basa samun taimakon kayan abinci da kuma magunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.