Afghanistan-Taliban

Taliban ta tsananta kai hare-hare yankin 'yan kabilar Hazaras

A baya-bayan nan ne dai Taliban ta amince da shiga wata tattaunawar zaman lafiya tsakaninta da gwamnatin ta Afghanistan karkashin jagorancin Rasha.
A baya-bayan nan ne dai Taliban ta amince da shiga wata tattaunawar zaman lafiya tsakaninta da gwamnatin ta Afghanistan karkashin jagorancin Rasha. AP

Rahotanni Daga kasar Afghanistan sun ce an samu karuwar kai hare hare daga kungiyar Taliban a Yankin da 'yan kabilar Hazaras tsiraru su ke, yayin da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Zalmay Khalizad ya isa yankin domin shawo kan kungiyar ta rungumi zaman lafiya.

Talla

Kakakin 'yan Sandan Yankin, Ahmad Khan Sirat ya ce wani fada da ya barke da asubahin jiya a Yankin Ghazni, ya haifar da kashe 'yan Tawaye 15 da sojojin gwamnati 10, yayin da wasu 6 suka jikkata.

Kakakin kungiyar Taliban Zabiullah Mujahid ya bayyana cewa sojojin gwamnati 22 suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.