Yemen

Ana dab da kawo karshen rikicin Yemen

Wasu daga cikin mayakan da ke goyon bayan gwamnati a rikicin Yemen da ya lakume rayukan jama'a da dama
Wasu daga cikin mayakan da ke goyon bayan gwamnati a rikicin Yemen da ya lakume rayukan jama'a da dama STRINGER / AFP

An zafafa yunkurin kawo karshen rikicin Yemen, in da a yanzu bangarorin gwamnati da na ‘yan tawaye ke dab da zaman tattaunawar sulhu a tskaninsu, yayin da Birtaniya ta shige gaba a Zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don ganin an gaggauta cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Wannan na zuwa ne gabanin ziyarar da manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths zai kai Yemen da zummar shawo kan masu rikicin don ganin sun amince da zama a teburin sulhu tare.

Tuni shugaban ‘yan tawayen Huthi kuma jigo a siyasar Yemen, Mohammed Ali al-Huthi, ya bukaci mabiyansa da su dakatar da duk wani aikin soji tare da kawo karshen harba makamai masu linzami kan Saudiya.

Ita ma Saudiya da ke jagorantar hadakar rundunar da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ta nuna amincewarta da sabuwar tattaunawar sulhun.

dai wasu rahotanni na cewa, an samu barkewar kazamin tashin hankali tsakanin ‘yan tawayen da kuma dakarun da ke mara wa gwamnati baya a birnin Hodeidah a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.