Japan-Nissan

Kamfanin Nissan ya kada kuri'ar sallamar shugabansa kan almundahana

Nissan na zargin Ghosn da rufa-rufa wajen bayyana gaskiyar albashinsa tare kuma da amfani da kadarorin kamfanin wajen gudanar da wasu ayyuka na kashin kansa.
Nissan na zargin Ghosn da rufa-rufa wajen bayyana gaskiyar albashinsa tare kuma da amfani da kadarorin kamfanin wajen gudanar da wasu ayyuka na kashin kansa. JOEL SAGET / AFP

Majalisar Zastaswar Kamfanin Kera Motocin Nissan ta kada kuri’ar sallamar shugaban kamfanin, Carlos Ghosn bayan zargin sa da facaka da kudaden kamfanin, abin da ya sa aka cafke shi a Japan.

Talla

Kamfanin Nissan na zargin Ghosn da rufa-rufa wajen bayyana gaskiyar albashinsa tare kuma da amfani da kadarorin kamfanin wajen gudanar da wasu ayyuka na kashin kansa.

Sai dai ana ganin matakin sallamarsa na da nasaba da kokarin Nissan na maido da karsashinsa a hadakarsa da Renault da Mitsubishi da dukkanisu ke karkashin ikon Mr. Ghosn a can baya.

Ghosn mai shekaru 64, shi ne wanda ya yi silar kulla zumunci tsakanin kamfanionin uku.

A gefe guda, Majalisar Zartaswar Nissan ta kada kuri’ar sauke wani na hannun daman Ghosn, Greg Kelly kamar yadda jaridar Nikkie ta rawaito a Japan.

Yanzu haka mutanen biyu na ci gaba da kasancewa a hannun jami’an tsaro a birnin Tokyo.

Shi ma dai Mitsubishi zai yi wani taro a makon gobe don tattaunawa kan makomar Mr.Ghosn, yayinda tuni Renault ya ce, zai nada mataimakin shugaban rikon kwarya don ci gaba da jagorancin ragamarsa.

Daga cikin laifukan da ake zargin Ghosn da aikatawa sun hada da cike takardun bogi don karbar kudade, laifin da ka iya kai shi ga zaman gidan kaso na tsawon shekaru 10 tare da cin tarar sa Yuan Miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI