China-Kimiyya

Ikirarin kirkirar tagwaye ya haddasa muhawara mai zafi a duniyar kimiyya

Tuni dai wata tawaga da ta kunshi kwararrun masana kimiyya 122 na kasar China suka rattaba hannu kan takardar yin tir da wannan bincike, tare da bayyana shi a matsayin hauka.
Tuni dai wata tawaga da ta kunshi kwararrun masana kimiyya 122 na kasar China suka rattaba hannu kan takardar yin tir da wannan bincike, tare da bayyana shi a matsayin hauka. REUTERS/Stringe

Asibitin Shenzhen Harmonicare da ke China ya musanta zargin da ake masa na bayar da damar gudanar da aikin jirkita kwayoyin halittar dan adam domin samar da wasu jarirai irinsu na farko a duniya.Asibitin ya kuma ce takardar da ake ikirarin ya sanya hannu akai, don bada damar gudanar da binciken ta bogi ce.

Talla

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani Farfesa a kasar ta China He Jiankui, ya yi ikirarin samun nasarar yin amfani da ilimin kimiyya wajen jirkita kwayoyin halittar wasu jarirai mata biyu tagwaye domin basu kariya daga kamuwa da kwayar cutar HIV.

Sai dai ikirarin na Farfesa Jiankui ya jawo ce-ce-ku-ce a duniyar masana ilimin kimiyya, wadanda baya ga bayyana shakku kan sahihancin ikirarin, masanan sun kuma bayyana binciken jirkitar kwayoyin halittar na dan adam a matsayin abinda ya sabawa ka’ida.

Tuni dai wata tawaga da ta kunshi kwararrun masana kimiyya 122 na kasar China suka rattaba hannu kan takardar yin tir da wannan bincike, tare da bayyana shi a matsayin hauka, zalika sun kuma ce babu adalci a tattare da duk wani masanin kimiyya da ya yi yunkurin dulmiya cikin fagen na jirkita kwayoyin halitttar dan adam domin samar da wani jinsi na dabam.

A shekarar da ta gabata dai wani kwararren Likita dan kasar Italiya Sergio Cannavero, ya haddasa muhawara mai zafi a duniyar kimiyya, bayan ikirarin samun nasarar gudanar da dashen kan da adam na farko a tarihi a wani asibitin kasar CHina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.