An soma taron sasanta rikicin kasar Yemen
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yau ake soma taron sasanta rikicin kasar Yemen a Sweden wanda zai kunshi wakilan ‘Yan Tawayen Houthi da na gwamnati, domin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 4 ana fafatawa.
Taron, wanda zai gudana a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, shi ne irin sa na farko tun shekarar 2016 lokacin da wani yunkurin gudanar da makamancinsa ya ruguje.
Majiyar Majalisar Dinkin Duniya tace matakin farko a taron, shi ne na ganin wakilan bangarorin biyu sun amince da juna kafin soma tattaunawa matsalolin da suka addabi kasar.
Yakin da aka shafe shekaru 4 ana gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen Houthi da rundunar hadin gwiwa ta wasu kasashen larabawa da Saudiya ke jagoranta, ya lakume rayukan mutane akalla 100,000, tare da kuma jefa mutane miliyan 14 cikin bala’in yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu