Saudiya

Saudiya ta ki mikawa Turkiya wadanda ake zargi da kisan Kashoggi

Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir.
Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir. AFP/file photo

Saudiya tace ba za ta mika ‘yan kasar domin yi musu shari’a kan kisan gillar da aka yiwa dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancinta dake kasar Turkiya ba, kamar yadda shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bukata.

Talla

Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubair, yace basa mika yan kasarsu zuwa wata kasa a irin wannan yanayi.

Shugaba Erdogan ya dade yana bukatar mika wadanda ake zargi domin ganin sun fuskanci shari’a amma abin yaci tura.

An hallaka Khashoggi ne ranar 2 ga watan Oktoba a ofishin Jakadancin Saudiya dake Santanbul, babban birnin Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI