Syria

Mun murkushe kungiyar ISIS a Syria - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump tare da wasu sojin kasar.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da wasu sojin kasar. REUTERS

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana samun gagarumar nasara akan kungiyar ISIS, inda ya ce zai janye dakarun kasar dake Syria.

Talla

Matakin shugaban dai yaci karo da manufar Amurka a Syria da kuma Yankin Gabas ta Tsakiya baki daya, abinda ya jefa ‘yan majalisun kasar, ma’aikatar tsaro, kasashen da ke kawance da Amurka, da kuma mayakan sa kai da ta ke marawa baya cikin kokwanto.

Yayin da yake ikirarin samun galaba kan kungiyar ta ISIS, shugaba Trump ya ce nasarar da suka samu, shi ya bada damar soma shirin janye dakarun Amurka zuwa gida, wanda ya ke da yakinin cewa abinda Amurkawa ke bukata kenan.

Matakin na Amurka zai yi tasiri a siyasar kasashen duniya, tare da diga ayar tambaya kan makomar mayakan Kurdawa da Amurka ke marawa baya, wadanda suka dade suna gwabzawa da Kungiyar ta ISIS.

A halin yanzu dai akalla dakarun Amurka 2000 ke cikin Syria, kuma dakarun sa kai da dama masu yaki a kasar da ke kawance da Amurka karkashin kungiyar SDF, yawancinsu Kurdawa ne, wadanda Turkiyya ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI