Indonesia

Aman wutar dutse ya hallaka mutane 222 cikin kwana 1 a Indonesia

Wasu bayanann kwararru na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu a Ibtila’in ka iya karuwa a dai dai lokacin da jami’an agaji ke ci gaba da kai dauki.
Wasu bayanann kwararru na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu a Ibtila’in ka iya karuwa a dai dai lokacin da jami’an agaji ke ci gaba da kai dauki. AFP

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwan da ta samo asali sanadiyyar aman wutar dutsen tsibirin Krakatoa a Indonesia yanzu haka ya kai mutane 222 yau Lahadi.

Talla

Tun da misalin karfe 9 na daren jiya Asabar ne ambaliyar ta afkawa yankunan Kudancin Sumatra da Java inda nan ta ke ta hallaka mutane kusan 50 baya ga jikkata wasu 600.

Wasu bayanann kwararru na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu a Ibtila’in ka iya karuwa a dai dai lokacin da jami’an agaji ke ci gaba da kai dauki.

Ko a shekarar 2004 ma wata mummunar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 a ma’aunin Richter a yankin Sumatra da ke yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar rayukan akalla mutane dubu 220,000 da ke zaune a yankunan da ke gaf da tekun India, dubu 168,000 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

Binciken kwararru ya tabbatar da cewa Indonesia ta fi kowace kasa fuskantar hadarin aukuwar girgizar kasa, aman wuta daga tsaunuka da kuma ambaliya a wasu lokutan, kasancewar ta a yankin Pacific, wadda daga karkashinsa aka fi samun yawaitar motsawar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI