Indonesia

Aman wutar tsauni ya haddasa ambaliyar tsunami a Indonesia

Tsaunin Anak Krakatoa, da ya haddasa ambaliyar Tsunami a Indonesia.
Tsaunin Anak Krakatoa, da ya haddasa ambaliyar Tsunami a Indonesia. Phys.org

Jami’an ceto a Indonesia, sun ce akalla mutane 43 sun mutu wasu kusan 600 kuma sun jikkata, sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa da ya aukawa yankin Krakatoa.

Talla

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar, ta ce aman wutar da wuni dutse ya yi ne ya haddasa ambaliyar ta tsunami, wadda ta afkawa yankunan Kudancin Sumatra da Java da misalin karfe 9 na daren jiya agogon kasar ba tare da an Ankara ba.

A shekarar 1883, dutsen da ke tsibirin na Krakatoa, ya taba yin aman wutar da ya haddasa tarwatsewar sassansa hade da toka da hayaki da suka watsu zuwa tafiya mai nisan sama da kilomita 20, lamarin da ya haddasa mutuwar sama da mutane dubu 36.

Binciken kwararru ya tabbatar da cewa Indonesia ta fi kowace kasa fuskantar hadarin aukuwar girgizar kasa, aman wuta daga tsaunuka da kuma ambaliya a wasu lokutan, kasancewar ta a yankin Pacific, wadda daga karkashinsa aka fi samun yawaitar motsawar kasa.

A shekarar 2004, wata gagarumar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 a ma’aunin Richter ta haddasa daga yankin Sumatra da ke yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar akalla mutane dubu 220,000 da ke zaune a yankunan da ke gaf da tekun India, dubu 168,000 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI