Afghanistan

Harin Afghanistan ya kashe mutane 43

An girke jami'an tsaro bayan harin na birnin Kabul
An girke jami'an tsaro bayan harin na birnin Kabul REUTERS/Omar Sobhani

Akalla mutane 43 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani ginin gwamnati da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan a ranar Litinin.

Talla

Rahotanni sun ce da farko maharan sun tarwatsa wata mota ce da aka shake da bama-bamai, kafin daga bisani su buda wuta a kan ginin ma’aikatar manyan ayyuka da ke birnin na Kabul.

Ma’aikatar Lafiya ta bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da aka kai wa birnin cikin wannan shekara da ke daf da kawo karshe.

Kawo yanzu babu wata kungiyar ‘yan tawaye da ta dauki alhakin kaddamar da farmakin, yayin da mai magana da yawun kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, ba su da hannu a kazamin harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI