Syria-Daular Larabawa

Daular larabawa ta sake bude Ofishin jakadancinta a Syria

Matakin sake bude Ofishin jakadancin na Daular Larabawa a Damascus wani yunkuri ne ganin Syria ta dawo hayyacinta tare da ci gaba da hulda da takwarorinta kasashen Larabawa.
Matakin sake bude Ofishin jakadancin na Daular Larabawa a Damascus wani yunkuri ne ganin Syria ta dawo hayyacinta tare da ci gaba da hulda da takwarorinta kasashen Larabawa. Reuters

Kasar Hadaddiyar daular Larabawa ta sanar da bude Ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus na Syria shekaru 7 bayan rufe shi a wani mataki na ganin kasar ta Syria ta dawo cikin takwarorinta kasashen Larabawa, bayan fuskantar yakin basasa na tsawon shekaru.

Talla

Tuni shugaba Bashar al-Assad ya yi maraba da matakin na Hadaddiyar daular Larabawa, batun da ke nuna cewa maktan kasashen sun fara aminta da kawo karshen yakin kasar na shekaru 7 da ya tilasta kulle ofisoshin jakadancin kasashe da ke Damascus babban birnin Syria.

Tun a watan Fabarairun shekarar 2012 ne Hadaddiyar Dalar Larabawa ta katse hulda da Syria bayan boren da al’ummar kasar suka rika yi ta neman hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad wadda ta kai ga barkewar yaki.

Yayin taron da ya gudana yau karkashin jagorancin jakadan Diflomasiyyar kasashen biyu sun daga tutar kasar ta Hadaddiyar Daular larabawa a birnin Damascus yayinda suka sanya hannu kan takardun fara aiki gadan-gadan.

Ana ganin dai matakin bude Ofishin da kuma ziyarar shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a kasar ta Syria wani mataki ne da hadakar kasashen larabawa ke kokarin dauka na ganin sun farfado da martabar kasar wadda ta fuskanci yakin shekaru bakwai da aka yi ittifakin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane dubu 360 yayinda wasu miliyoyi suka yi kaura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI