Saudiya

Saudiya ta yi garambawul a majalisar ministocinta

Sarkin Saudiya Salman bin Abdul'aziz.
Sarkin Saudiya Salman bin Abdul'aziz. Reuters/路透社

Sarki Salman na saudiya ya yi umarnin garambawul a majalisar ministocin kasar baya ga bangaren tsaro da kuma wasu masu rike da mukaman siyasa, sakamakon kakkausar sukar da kasar ke fuskanta daga kasashen duniya sanadiyyar kisan Dan jarida Jamal Khashoggi.

Talla

Cikin wadanda garambawul din ya shafa har da ministan harkokin waje da na yada labarai da shugaban hukumar tsaron cikin gida da na hukumar yawon bude ido.

A bangare guda garambawul din na sarki Salman ya gaza tabo ma’aikatar kudi da ta makamashi duk kuwa da halin da tattalin arzikin kasar ya tsunduma sanadiyyar caccakar bayan kisan Khashoggi.

Yanzu haka dai umarnin na sarki Salman na nuna cewa, tsohon ministan kudin kasar Ibrahim al-Assaf wanda aka kame bara cikin wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa zai maye gurbin Adel al-Jubeir a matsayin ministan harkokin waje.

Sauran da garambawul din ya shafa, akwai Yarima Abdullah bin Bandar da zai rike mukamin shugaban hukumar tsaro ta cikin gida yayinda Musaed al-Aiban zai zama babban bai ba da shawara kan harkokin tsaro na Saudiyan.

Haka zalika akwai kuma Turki al-Shabanah wanda aka nada a matsayin ministan yada labarai inda yam aye gurbin Awwad al-Awwad wanda yanzu ya koma babban mashawarcin fadar mulkin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI