Bangladesh

Sheikh Hasin na kan hanyar lashe zaben Bangladesh

Sheikh Hasin Firaministar Bangladesh
Sheikh Hasin Firaministar Bangladesh Sangbad Sangstha/Handout via REUTERS

Firaministar Bangladesh Sheikh Hasin ta lashe zaben yan majlisun kasar da ya gudana yau lahadi, a cewar sakamakon farko.Gungun masu dafawa Sheikh Hasina ne suka lashe yawan kujeru a majalisar kasar, a dai dai lokacin da jam’iyyun adawa ke bayyana cewa an tafka magudi a zaben da ya haddasa mutuwar mutane 17.

Talla

Gungun masu marawa Firaministar sun lashe akalla kujeru 191 daga cikin kujeru 300 na majlisar, wanda hakan ya zarce adadin 151 dake bayar da damar samun rijaye a zauren majalisar.

Sheikh Hasin mai shekaru 71 da kuma ta share shekaru goma ta na jagorantar gwamnatin kasar ta Bangladesh na kan hanyar sake samun wa’adi na hudu a wannan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.