Myanmar-Rakhine

Tsagerun kungiyar AA sun farmaki Ofisoshin 'yansanda 4 a Myanmar

Cikin makwanni biyun da suka gabata ne rundunar Sojin Myanmar ta shigo da 'yansanda cikin yakin da ta ke da tsageru daga kungiyoyi daban-daban ciki har da ta tsagerun na AA.
Cikin makwanni biyun da suka gabata ne rundunar Sojin Myanmar ta shigo da 'yansanda cikin yakin da ta ke da tsageru daga kungiyoyi daban-daban ciki har da ta tsagerun na AA. AFP/Ye Aung Thu

Wata kungiyar 'Yan tawaye a jihar Rakhine da ke kudancin kasar Myanmar ta kaddamar da hare-hare kan wasu Ofisoshin ‘yan sanda 4 da ke gab da iyakar kasar da Bangladesh tare hallaka mutane 7 baya ga daukar wasu 14 a matsayin fursunonin yaki.

Talla

Harin wanda rundunar Sojin kasar ta bakin kakakinta Birgediya Janar Zaw Min Tun ta tabbatar da shi, ta ce wata kungiyar ‘yan tawaye da ake yiwa lakabi da Arakan Army AA ce ta kaddamar da shi.

Kungiyar ta AA wadda a baya-bayan nan ta tsananta kai hare-hare a yankin da ya yi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da na addini na neman lallai gwamnatin Myanmar ta samar da kwarya-kwaryan 'yanci ga yankin na mabiya addinin Budda.

Cikin sanarwar da kungiyar ta AA ta fitar ta ce ta hallaka makiyanta 7 yayinda ta dauki wasu a matsayin fursunan yaki baya ga raunata wasu, ta ce lokaci ya yi da ya kamata yankin ya samu kwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kansa.

Ko a bara ma dai rikicin kabilancin da al'ummar jihar ta Rakhine suka assasa ya haddasa kisan tarin masulmi 'yan kabilar Rohingya baya ga tilastawa kusan miliyan guda tserewa daga kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI