Syria

Turkiya ta yaba da janyewar dakarun Amurka daga Syria

Sansanin yan gudun hijira a kan iyaka da Turkiya da Syria
Sansanin yan gudun hijira a kan iyaka da Turkiya da Syria AFP Photos/ Omar Haj Kadour

Turkiya ta yaba da jawabin sakatary harakokin wajen Amurka Mike Pompeo dangane da hukunrin kasar na kare kan iyakokin ta daga hare-haren mayakan jihadi bayan ficewar dakarun Amurka daga Syria.

Talla

Ministan harakokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya bayyana haka a yayin da yake gabatar da jawabi a kudancin kasar.

Ficewar dakarun Amurka daga Syria zai haddasawa dakarun Kurdawa koma baya, kasancewar sun shafe lokaci suna aiki kafada da kafada da sojin Amurka wajen yakar mayakan ISIS, yayinda Turkiya ke yi musu kallon yan tawaye da ya dace ta yaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.