Mayakan Houthi na samun tallafi daga cinikin man Iran - MDD
Wallafawa ranar:
Wani rahoton majalisar dinkin duniya, ya ce ‘yan tawayen Houthi dake gwabza yaki da dakarun kasashen Larabawa a Yemen, na samun kudaden tallafi daga man fetur din kasar Iran.
Bayanin na kunshe cikin rahoton bincike mai shafuka 85 kan yakin Yemen na shekarar 2018, da wata tawagar majalisar dinkin duniya ta gudanar.
Rahoton ya ce ana yi wa tarin man fetur din da ake fasa kaurinsa daga kasar Iran zuwa mayakan na Houthi takardun jabu, don kaucewa binciken masu sa ‘ido na majalisar dinkin duniya, inda ‘yan tawayen ke samun akalla dala miliyan 30 daga cinikinsa.
Sai dai Iran na ci gaba da musanta zargin cewa tana taimakawa ‘yan tawayen na Houthi ta fuskar soji, wadanda suka kwace iko da babban birnin Yemen Sana’a, a shekarar 2014, abinda ya haifar da kazamin yakin kokarin murkushe su, da dakarun wasu kasashen Larabawa ke yi, bisa jagorancin Saudiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu