Syria

An kaddamar da farmaki kan kauyen da ya rage a karkashin ISIS

Wasu dakarun 'yan tawayen Syria da ke yakar kungiyar ISIS tare da hadin gwiwar mayakan Kurdawan YPG da Amurka ke marawa baya.
Wasu dakarun 'yan tawayen Syria da ke yakar kungiyar ISIS tare da hadin gwiwar mayakan Kurdawan YPG da Amurka ke marawa baya. Rodi Said/Reuters

Mayakan kurdawan YPG da ke samun goyon bayan Amurka a Syria, sun kaddamar da farmakin karshen kan mayakan ISIS, da suka ja tunga a kauyen Baghouz, yanki na karshe dake karkashinsu a gabashin kasar ta Syria.

Talla

An Kaddamar da farmakin a jiya Asabar, bayan kwashe sama da fararen hula dubu 20 daga kauyen na Baghouz da ke lardin Dier Az Zor.

Amurka da dakarun kawancenta na Kurdawa, na fatan kawo karshen wanzuwar mayakan na ISIS a Syria bayan kammala farmakin na baya bayan nan.

Kakakin gamayyar mayakan Kurdawa da na ‘yan tawayen Syria da Amurka ke marawa baya, Mustafa Bali, ya ce yawan mayakan ISIS da ke kauyen na Baghouz, zai iya kaiwa 600, zalika akwai ragowar fararen hular da basu samu damar tserewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.