Asiya

Mutane kusan 20 ne suka mutu a wani harin Bam a Pakistan

Akalla mutane 20 suka mutu yayinda wasu fiye da 40 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake yau a kasuwar garin Quetta mai cike da jama’a da ke yankin Baloutchistan dake kasar Pakistan.

Yankin da harin Bam ya wakana a Pakistan
Yankin da harin Bam ya wakana a Pakistan REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

A cewar Ministan cikin gidan kasar Pakistan ,biyu daga cikin mutanen da harin ya rutsa dea su yara kanana ne.

Rahotanni sun ce galibin wadanda harin ya rutsa da su mabiya shi’a ne lokacin da su ke tsaka da hada-hadar saye da sayarwa a kasuwar wadda ta shahara wajen sayar da kayan lambu da na marmari.

Ana zargin yan Taliban da kai wannan kazamin hari,yayinda Babban jami’I mai kula da harkokin tsaro na garin, ya ce tuni aka isar da wadanda suka raunata a harin asibiti.

Yankin Baloutchistan dake kan iyaka da kasar Iran,da Afghanistan na daga cikin yankuna na kasar da hare-haren ta’addanci ya tagayyara .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI