Afghanistan-Taliban

Wakilan Afghanistan 250 za su gana da wakilan Taliban a Doha

Wakilan kungiyar Taliban a ganawarsu da wakilan Amurka domin tattaunawar sasanta rikicin kasar Afghanistan a birnin Doha na Qatar
Wakilan kungiyar Taliban a ganawarsu da wakilan Amurka domin tattaunawar sasanta rikicin kasar Afghanistan a birnin Doha na Qatar Qatari Foreign Ministry/Handout via REUTERS

Gwamnatin Kasar Afghanistan ta bayyana jerin sunayen wakilan ta da za su gana da wakilan kungiyar Taliban a taron sasanta rikicin kasar da zai gudana a Doha a cikin wannan mako.

Talla

Jerin sunayen wakilan gwamnatin 250 da fadar shugaban kasa ta gabatar, ya sanya sunayen babban hafsa a fadar shugaban kasa Ashraf Ghani, wato Abdul Salam Rahimi da Amrullah Salah, tsohon shugaban hukumar liken asiri.

A baya dai kungiyar Taliban ta ki ganawa da wakilan gwamnati yayin da ta ke tattaunawa da wakilan gwamnatin Amurka kan kawo karshen yakin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.