Pakistan-Ta'addanci

'Yan bindiga sun harbe Fasinja 14 a Pakistan

Wani harin kunar bakin wake a Pakistan
Wani harin kunar bakin wake a Pakistan REUTERS/Mukesh Gupta

Wasu ‘yan bindiga a kasar Pakistan sun hallaka Fasinjojin motar Safa 14 lokacin da su ke tsaka da tafiya a lardin Balochistan yau Alhamis.

Talla

Sakataren harkokin Lardin Haider Ali, da ke tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar su fiye da 12 sun je sanye da kayan soji a jikinsu, matakin da ya basu damar iya tsayar da motar cikin sauki.

A cewar Haider, cikin mutane 14 da ‘yan bindigar suka kashe dukkaninsu ‘yan kasar Pakistan har da Jami’in sojin ruwan kasar guda da kuma wani Soji.

Sanarwar da Ministan cikin gida, Mr Zia Langov ya fitar ta nuna cewa mutanen 14 da ‘yan bindigar suka tsamo daga motoci na kan hanyarsu ne ta zuwa Karachi daga garin Ormara.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, wanda ke zuwa kasa da mako guda bayan harin kunar bakin wake a Quetta da ya hallaka mutane 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.