Shugaba Kim zai gana da Vladmir Poutine na Rasha
Wallafawa ranar:
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai kai ziyara a Rasha don ganawa da shugaba Vladimir Putin cikin wannan wata, alamar da ke nufin cewa Rasha na son shiga a dama da ita a shirin nukiliyar kasar ta Koriya,shirin ya haifar cda caccar baka tsakanin kasar ta Koriya da wasu kasashen Duniya.
Shugaba Kim ya ce zai ziyarci Moscow ne jim kadan bayan da ya bukaci Amurka ta cire sunan sakataren harkokin waje Mike Pompeo daga cikin tawagar da ke tattaunawa kan wannan batu, saboda ba ya da kwarewa a cewar Koriya.
Da jimawa Amurka ta sha nuna damuwa tareda yin kashedi zuwa Shugaba Kim Jong Un traeda bukatar ganin ya lalata duk wasun makamai da kasar keda su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu