Srilanka

Jerin hare-haren bom sun hallaka mutane 207 a Sri Lanka

Guda cikin Majami'un da aka kaddamar da farmakin a kasar Sri Lanka
Guda cikin Majami'un da aka kaddamar da farmakin a kasar Sri Lanka ISHARA S. KODIKARA/AFP

Akalla mutane 207 aka tabbatar da mutuwarsu, bayan tashin wasu bama-bamai har 8 a wasu majami’u da Otel a kasar Sri Lanka ciki har da ‘yan kasashen ketare 35.Harin wanda yanzu haka ya jikkata kusan mutane 500, ya faru ne lokacin da ake tsaka da bukukuwan Easter, a kasar ta Sri Lanka.

Talla

Cikin mutanen da suka mutu a harin bama-baman na Majami’u da Otel har da tarin ‘yan kasashen ketare, galibi wadanda suka shiga kasar don gudanar da bukuwan Easter.

Tuni dai Firaminista Ranil Wickremesinghe ya yi umarnin sanya dokar takaita zirga-zirga a ilahirin sassan kasar mai yawan al'umma miliyan 21, bayan hare-haren wanda ya ce shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan kawo karshen yakin basasarta shekaru 10 da suka gabata.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta Sri Lanka ta ce, bama-bamai biyu wadanda su tashi a daga karshe, wasu 'yan kunar bakin wake ne, suka tayar da bom din da ke jikinsu a wani katafaren Otel da ke babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Sri Lanka ya ruwaito cikin 'yan kasashen ketare da harin ya rutsa da su har da Amurka da 'yan Netherland da 'yan Birtaniya da wani dan Portugal ka na wani dan Japan da ya jikkata.

A cewar rundunar 'yan sandan kasar, yanzu haka akwai, gawarwakin wasu mutane 27 wadanda ake kyautata zaton maharan ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI