Sabuwaar girgizar kasa ta hallaka mutane 5 a Philippine
Wallafawa ranar:
Akalla Mutane 5 sun mutu sakamakon rugujewar gine-gine 2 sanadiyyar wata kakkarfar girgizar kasa da ta dirarwa wani yanki na kasar Philippines.
Rahotanni sun ce an yi nasarar zaro mutane 3 da ginin ya danne su a kauyen Porac, haka zalika wata tsohuwa da jikanta wadanda suma wani ginin na daban ya hallaka a Lubao.
Gwamnan yankin Pampanga da ya fuskanci girgizar kasar Lilia Pineda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni jami’an agaji suka shiga aikin ceto.
A cewar Gwamnar tun da tsakaddaren jiya ne girgizar kasar ta fara wadda ta ce ta haddasa tsoro a zukatan al’ummar yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu