Pakistan-Iran

Pakistan da Iran za su kafa rundunar bayar da tsaro akan iyakokinsu

Shugaban Iran Hassan Rouhani tare da Firaministan Pakistan Imran Khan a Tehran
Shugaban Iran Hassan Rouhani tare da Firaministan Pakistan Imran Khan a Tehran © Reuters

Kasashen Iran da Pakistan sun amince da kafa wata rundunar hadin gwuiwa da za ta dinga kai daukin gaggawa akan iyakokin da ke tsakanin su idan bukatar hakan ta taso, bayan kazamin harin da aka samu kan jami’an tsaro.

Talla

Bayan wata ganawa da shugabanin kasashen biyu Hassan Rouhani da Imran Khan suka yi a Tehran, shugaban Iran ya ce sun amince da shirin kafa rundunar ne domin yaki da Yan ta’adda.

Firaministan Khan ya ce manyan jami’an tsaron kasashen biyu za su zauna domin tsara yadda za su gudanar da aikin.

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan bindiga da rahotanni ke nuna cewa sun shiga kasar ta Pakistan ne daga Iran suka farmaki wasu motocin safa tare da hallaka tarin jami'an tsaro.

Baya ga karancin tsaro a cikin gida Pakistan ke fuskanta sake sukurkucewar alaka tsakaninta da makociyarta India a baya bayan nan babban kalubale ne a gareta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.