Sri Lanka

'Yan sandan Sri Lanka sun hallaka mayakan IS 15 a farmaki kan maboyarsu

Jami'an tsaro a Sri Lanka bayan tsauraran matakan tsaro sanadiyyar harin ranar lahadi
Jami'an tsaro a Sri Lanka bayan tsauraran matakan tsaro sanadiyyar harin ranar lahadi ©REUTERS/Dinuka Liyanawatte

Rundunar ‘yan sanda Sri Lanka ta tabbatar da kisan mayakan IS akalla 15 a wani farmaki da ta kai maboyarsu a kasar, farmakin da ke matsayin martinin kan harin ranar Easter da ya hallaka mutane kusan 300.

Talla

Yayin farmakin jami’an ‘yan sandan su shaidawa manema labarai cewa, wasu mutane 3 da ake kyautata zaton mayakan IS ne tashi Bom a jikinsu, don gudun kama su, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu tare da wasu kananan yara 6.

A cewar rundunar jami’anta sun harbe wasu karin mayakan na IS 12 nan take, lokacin da suka yi kokarin farmakarsu, yayin sumamen wanda ya gudana tsakaddaren jiya wayewar yau Asabar.

A lahadin da ta gabata ne dai wasu hare-hare da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa ya hallaka kusan mutane 300 bayan tashin bama-bamai har 8 ciki har da na kunar bakin wake 2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI