India

Dalibai 20 sun kashe kansu saboda faduwa jarabawa a India

Wata tawagar dalibai a India
Wata tawagar dalibai a India ©Reuters.

Rahotanni daga India na cewa akalla dalibai 20 sun hallaka kansu har lahira bayan fitar da sakamakon jarabawar BIE ta makarantun gaba da sakandire, wadda aka zubar da tarin dalibai saboda rashin kwazo.

Talla

Guda cikin daliban Sirisha Rao ta zazzagawa kanta fetur tare da bankawa kanta wuta a cikin gidansu bayan sanar da ita rashin nasara a jarabawar Biology wadda sai da ita ne za ta iya samun gurbi a matakin jami’a.

Wata majiyar tsaro a kasar ta ce cikin mako guda dalibai fiye da 20 sun kashe kansu saboda takaicin rashin nasara a jarabawar, wadda kimanin dalibai miliyan guda suka zana amma kuma dalibai dubu dari 350 suka fadi.

Yawan adadin daliban da suka fadi a jarabawar da kuma yawaitar fuskantar kashe kan a sassan kasar ya tilastawa Kungiyoyin Dalibai da ma iyaye baya ga kungiyoyin kare hakkin dan adam fantsama zanga-zanga.

Tuni dai Babban Minista a kasar ta India da ta yi kaurin suna wajen dabi’ar kashe kai K.Chandrashekhar Rao ya yi umarnin gaggauta sake bibiyar sakamakon jarabawar inda ya bukaci daliban da su daina daukar matakin kashe kansu.

Yanzu haka dai cibiyoyin hukumar ta BIE 12 na aikin bibiyar sakamakon daliban da suka fadi a jarabawar don tantancewa.

Ka zalika kungiyar Dalibai a kasar ta Indiya ta bukaci biyan diyyar duk dalibin da ya kashe kansa sanadiyyar dauwa jarabawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.