Afghanistan-Taliban

Ba za mu amince da matsayar da aka cimma a taron Loya Jirga ba-Taliban

Shugaban sashen siyasar kungiyar Taliban Sher Mohammad Abbas Stanakzai
Shugaban sashen siyasar kungiyar Taliban Sher Mohammad Abbas Stanakzai REUTERS/Maxim Shemetov

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta yi ikirarin cewa baza ta amince da duk wata matsaya da za a cimma yayin Taron Loya Jirga da ke guda a birnin Kabul ba, taron da ke samun halartar jagorori daga bangaren Kabilu, Addini da kuma Siyasar kasar sama da mutum dubu uku.

Talla

Taron na Loya Jirga da za’a shafe kwanaki hudu ana yinsa, shi ne mafi girma a kasar ta Afghanistan kuma wani yunkuri ne na gwamnatin kasar wajen ganin ta yi tasiri a tattaunawar da ke gudana tsakan Amurka da mayakan Taliban don kawo karshen yakin shekaru 17.

Sai dai tuni kungiyar ta Taliban, ta sanar da kauracewa taron na Loya Jirga tare da shan alwashin watsi da duk wani mataki da aka yanke yayinsa wanda ake ganin baya rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin kungiyar da shugaba Ashraf Ghani.

Baya ga kungiyar ta Taliban a bangare guda wasu manyan yan siyasar kasar suma sun kauracewa taron bisa zargin shugaba Ghani da kokarin yin amfani da damar wajen cimma manufar siyasa.

An dai shafe sama da shekaru 100 ana gudanar da wannan taro na Loya Jirga a Afghanistan, lokaci zuwa lokaci, inda ake amfani da shi wajen warware manyan matsalolin da ke addabar kasar.

Makamancin taron da ya gudana a baya bayan nan dai shi ne na shekarar 2013, wanda ya baiwa sojojin Amurka damar ci gaba da zama a Afghanistan, bayan karewar wa’adin zamansu a shekarar 2014 da aka tsara da fari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI