Isa ga babban shafi
India

Guguwar Fani na ci gaba da karade yankunan India

Guguwar Fani ta tilasta wa mahukuntan India kwashe jama'a daga gidajensu
Guguwar Fani ta tilasta wa mahukuntan India kwashe jama'a daga gidajensu REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Abdoulkarim Ibrahim
1 Minti

Guguwar da masana suka yi wa lakabi da ‘’Fani’’ ta isa yankin gabar ruwan gabashin kasar India a safiyar yau juma’a, to sai dai tuni mahukunta suka fara kwashe jama’a kafin isar wannan guguwa da ke tare da ruwan sama.

Talla

Da misalin karfe 8 na safiyar yau agogon kasar ta India ne guguwar ta fara isa a yankin gabar ruwan gabashin kasar, inda tuni ta fara karya bishiyoyi da turakun wutar lantarki da kuma fargabar yiyuwar samun ambaliyar ruwa.

Masana sun ce, guguwar wadda aka jima ba a ga makamanciyarta ba, yanzu tana tafiyar kilomita 180 zuwa 200 a cikin sa’a daya, lamarin da ya sa mahukunta suka kwashe mutane daga yankuna 19 da ake zaton cewa za ta fi yin illa.

A yammacin jihar Bengal ne ake fargabar cewa guguwar za ta fi yin ta’adi, lamarin da ya sa mahukunta suka bayar da umarnin kwashe kusan mutane milyan daya zuwa wasu wurare da ke nesa ga gabar ruwan teku.

A shekarar 1999, an taba samun makamanciyar irin wannan guguwa, inda ta yi sanadiyyar mututwar sama da mutane dubu 10. Hasashe dai na nuni da cewa guguwar Fani za ta iya shafar makociyar kasar wato Bengladesh kafin gobe Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.