Myanmar

Gwamnatin Myanmar ta saki 'yan jaridun da ta daure

Wakilan kamfanin dillancin labarai na Reuters Wa Lone da Kyaw Soe Oo da gwamnatin Myanmar ta saki daga dauri.
Wakilan kamfanin dillancin labarai na Reuters Wa Lone da Kyaw Soe Oo da gwamnatin Myanmar ta saki daga dauri. Reuters/Ann Wang

Gwamnatin Myanmar ta saki wakilan kamfanin dillancin labarai na Reuters guda biyu da ta daure, bisa zarginsu da karya dokar yada labaran sirri da suka shafi gwamnati.

Talla

‘Yan Jaridun da suka hada da Wa Lone mai shekaru 33 da Kyaw Soe Oo mai shekaru 29, sun shafe sama da kwanaki 500 a gidan yari kafin shakar iskar ‘yanci.

Da fari dai wata kotun Myanmar ta yanke way an jaridun biyu hukuncin daurin shekaru 7 ne, bayanda jami’an tsaron kasar suka kamasu a watan Disamba na 2017, saboda binciken da suke gudanarwa kan yadda sojoji suka yiwa wasu Musulmi ‘yan kabilar Rohingya kisan gilla a jihar Rakhine.

Bayan sakin ‘yan jaridun biyu, gwamnatin Myanmar ta kuma sanar da cewa za ta saki wasu karin fursunoni dubu 6 da 520, a karkashin wani shirin afuwa da ta kirkiro.

Kaddamar da yaki kan wasu gungunmasu tada kayar baya a daga kabilar ta Rohingya a jihar Rakhine da sojoji suka yi a watan agustan 2017, ya tilastawa sama da ‘yan kabilar dubu 730 tserewa zuwa Bangladesh, domin kaucewa cin zarafi da kisan gillar da ake musu da sunan murkushe ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.