Kim na Korea ta Arewa ya yi umarnin karfafa sashen Nukiliyar kasar
Wallafawa ranar:
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un, ya baiwa rundunar sojin kasar, umarnin kara karfinta na harba manyan makamai masu linzami, tare da kuma bada umarnin sake gwajin wasu makaman da suka kera da suka dara na baya.
Matakin na shugaba Kim, ya biyo bayan kama wani jirgin dakon kayan kasar da Amurka ta yi dauke makamashin kwal, bisa zarginsa da karya ka’idojin takunkuman karya tattalin arzikin da ta kakaba mata, bisa amincewar majalisar dinkin duniya.
Ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Amurka da Korea ta Arewa, tun bayan gaza cimma matsayar da aka yi yayin tattaunawar shugaba Trump da Kim karo na biyu a birnin Hanoi na Vietnam, dangane da bukatar yin watsi shirinta na mallakar makaman Nukiliya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu