Asiya

An kama wasu mayakan jihadi a Indonesia

Yan Sanda masu yaki da ayukan ta'adanci a Indonesia
Yan Sanda masu yaki da ayukan ta'adanci a Indonesia REUTERS/Beawiharta

Yan sanda a Indonesia, sun sanar da cafke mutane 29 da ake zargin cewa suna da alaka da kungiyar IS, kuma wasu daga cikinsu na shirin kai hare-hare ne a cikin kasar.An kame mutanen 29 ne a cikin wannan wata, yayin da adadin wadanda aka kama bisa zargin ta’addanci ya kai mutane 60 a cikin wannan shekara.

Talla

Kasar ta Indonesia ta kasance kasa da yan kunar bakin wake suka jima suna kai munanan hare-hare tareda kisan farraren hula.

Wasu alkaluma sun nuna ta yada yan kunar bakin wake suka yawaita kai hare-hare zuwa mujami’u dake wasu biranen kasar ,kama daga Surabaya da sauren su.

Kakakin hukumar binciken sirri na kasar ta Indonesia Jemaah Ansharut Daulah ya ce akwai kyautata zaton kungiyar IS ce ke shirya wadanan hare-hare a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI