Isa ga babban shafi
Saudiya

Taron kawo karshen rikici tsakanin kasashen Larabawa

Wasu daga cikin masu fatan ganin an cimma zaman lafiya a kasashen larabawa
Wasu daga cikin masu fatan ganin an cimma zaman lafiya a kasashen larabawa HRW
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Kasar Saudiya a jiya asabar ta bukaci gani a shirya taro kasashen yankin Gulf da na Larabawa biyo bayan harin da gam-gam na lalata wasu daga cikin jiragen ruwa na jigilar mai da aka yi a yankin Gulf.

Talla

Tarurukan da Saudiya ke fatan ganin sun gudana ranar 30 ga wannan watan da muke cikin sa a kasar zai hada Shugabanin kasashen yankin da wasu na Larabawa.

Fatan hukumomin Saudiya shine na cimma matsaya daya wanda hakan zai taimaka da murya daya don cimma zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaro a kasashen su.

Saudiya a cewar Ministan harakokin wajen kasar Abdel Al Jubeir, kasar sa ba ta fatan ganin yaki ya barke tsakanin Iran da wata kasa,,banda hakan jami’in diflomasiyar ya bayyana cewa kasar sa za ta taka duk rawar da ta dace don kaucewa shiga yaki da Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.