India-Zabe

Firaminista Narendra Modi ya sake lashe zaben India

Firaminista Narendra Modi
Firaminista Narendra Modi REUTERS/Amit Dave

Sakamakon zaben India da ya fara fita yanzu haka ya nuna yadda jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ta lashe akalla kujeru 300 cikin kujeru 543 da aka zabe yayin zaben akasar da aka shafe fiye da wata guda ana yi.

Talla

Tuni dai Firaminista Narendra Modi ya yi ikirarin lashe zaben da gagarumar nasara dai dai lokacin da hukumar zaben kasar ta India ta kirge rabi daga cikin kuri’u fiye da dubu dari 6 da aka kada.

Yanzu haka dai sakamakon zaben ya nuna yadda babbar jam’iyyar adawa ta Rahul Gandhi ta samo kujeru 49 kacal, yayinda BJP ke da kujeru 300.

A wani sakon Twitter da Narendra Modi ya wallafa a shafinsa, ya taya al’ummar kasar murna inda ya sha alwashin sake bunakasa ci gaba kasar ta fuskar tattalin arziki, fasaha kimiyya da kuma karfin fada aji a duniya.

Shima dai shugaban Jam’iyyar ta BJP Amit Shah ya aike da nasa sakon taya murnar, inda ya ce, sakamakon zaben ya nuna yadda Indiyawa suka damu da ci gabansu.

A nasa banagren Uday Kotak attajirin kasar ta India ya aike na nasa sakon taya murnar ga Firaminsta Narendra Modi, inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a sake gudanar da gagarumin sauyi da zai daga darajar ta India a Idon daniya, ta hanyar yakar rashin ayyukanyi da kuma bunkasa tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.