Indonesia

Rikici ya barke a Indonesia bayan sanar da sakamakon zabe

Akalla mutane 6 suka mutu sakamakon tarzomar da ta biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar Indonesia, wanda hukumar zabe ta tabbatar da cewar shugaba Joko Widodo ya samu nasara.

Shugaba Joko Widodo na Indonesia
Shugaba Joko Widodo na Indonesia Reuters
Talla

'Yan sanda sun yi ta dauki ba dadi da dubban masu zanga zangar rashin amincewa da sakamakon a birnin Jakarta, wadanda suka yi ta jifar jami’an tsaro da duwatsu, yayin da 'yan Sandan ke harba musu hayaki mai sa hawaye da harsashin roba.

Gwamnan Jakarta Anies Baswaden ya ce akalla mutane 200 suka jikkata a arangamar, yayin da shugaban 'yan Sanda ya ce an kama mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI